Connect with us

News in Hausa

Dattijon jamiyyar PDP Olabode George ya gargadi Tinubu kan yakar Nijar

Published

on

Tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar PDP na kasa Cif Olabode George, ya gargadi shugaba Bola Tinubu da ya yi tunani sosai kafin ya afkawa Jamhuriyar Nijar da yaki. A cikin wata wasika da yarubuta zuwa shugaban kasa a matsayinsa na “dan Najeriya, Janar mai ritaya a sojan Najeriya, mai kishin kasa kuma mai dabarar yaki,” George ya bayyana cewa yana da kyau shugaban ya ci gaba da harkokin diflomasiyya maimakon ya assasa “yakin da ba dole ba.”

Continue Reading
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

News in Hausa

Shin ko karfin siyasar ta Wike tasamu rauni?

Published

on

By

A cikin dama guda daya da Gwamnan Ribas Siminalaya Fubara ya samu:

1. Ya kori shugaban ma’aikata na fadar Gwamnatin jihar, wanda Wike ne ya nada shi.

2. Ya cire dukkan shugabannin kananan hukumomi guda ashirin da uku ba jihar baki daya, wanda duk Wike ne ya kawo su.

3. Ya rushe majalisar zartarwar jihar, wadda ta kunshi Kwamishinoni, wanda fiye da rabinsu Wike ne ya kawo su.

4. Ya canja Kakakin Majalisar dokokin jihar wanda shima Wike ne ya kawo shi.

5. Ya dakatar da babban jojin jihar wanda shima Wike ne ya kawo shi.

Wannan karamin misali ne na irin karfin da kujerar Gwamna ta ke da shi a Najeriya. Wike ya manta duk abinda yake yi saboda yana rike da kujerar Gwamnan ne, yau damar da ya samu yayi abinda yaga dama ita wani ya samu ya lalata masa siyasa cikin kankanin lokaci.

Wike ya tarawa kansa abokan fada da yawa, kuma ba zai iya ba. Domin da alama Sim Fubara ya kawo karshen tasirin da Wike yake ganin yana da shi a siyasar Najeriya. Kama-ta-dinu tu-danu.

Continue Reading

News in Hausa

Kotu za ta yanke hukunci a kan zaben gwamnan Kaduna

Published

on

By

Kotun sauraron kararrakin zaben gwamna da ke jihar Kaduna za ta yanke hukunci a yau Alhamis 28 ga Satumba, 2023.
Jaridar The Boss ta samu labarin cewa kotun zata zartar da hukuncinta ne ta hanyar Zoom, a inda zata ayyana hukunci kan karar da jam’iyyar PDP da dan takararta, Isah Mohammed Ashiru Kudan suka gabatar a gabanta na neman korar Uba Sani a matsayin gwamnan jihar. Sani ya kasance dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a lokacin zaben.
Jaridar The Boss zata kawo cikakkun bayanai daga baya…

Continue Reading

News in Hausa

Kungiyar Kwadago Zata Shiga Yajin Aikin Sai Baba Tagani

Published

on

By

Kungiyoyin kwadago na NLC da TUC ta sanar da kudirinda na shiga aikin sai baba tagani a ranar Talata mai zuwa 3 ga watan Oktoba 2023. Hakan ya biyo bayan zaman tattaunawa da shugabannin kungiyoyin sukayi a yau Talata a Abuja.
Daya daga cikin korafin kungiyoyin nada alaka da halin tsananin wahala da yan Najeriya suke ciki, da kuma gazawar gwamnatin tarayya bisa alkawarin kawo tsare-tsare na rage radadi ga al’umma.

Continue Reading

Trending