Shugaba Bola Tinubu ya aike da wasika ga majalisar dattawan kasar, inda ya nemi amincewar daukar matakin soji da sauran takunkumi kan jami’an sojin da sukayi juyin mulki a Nijar. Shugaban majalisar dattijai, Godswill Akpabio, ya karanta wasikar a zaman majalisar dattawan na yau Juma’a. Wasikar ta ce, “Baya ga abin takaici da yafaru a siyasar jamhuriyar Nijar da ya kai ga hambarar da shugabanta, kungiyar ECOWAS karkashin jagorancina ta yi Allah-wadai da juyin mulkin baki daya tare da kuduri aniyar neman dawo da zababben gwamnatin da aka zaba. A wani yunkuri na maido da zaman lafiya, ECOWAS ta kira taro tare da fitar da sanarwar kamar haka.
“Rufewa da sanya ido kan iyakokin Najeriya da Jamhuriyar Nijar.
”Katse wutar lantarki ga Jamhuriyar Nijar.
“Nemo tallafin ƙasashen duniya don aiwatar da duk matakan da ECOWAS ta dauka.
“Hana gudanar da zirga-zirgar jiragen sama na kasuwanci da na musamman a ciki da wajen Jamhuriyar Nijar.
“Katange kayayyakin da ake jigilarsu zuwa Nijar musamman daga Legas da tashoshin ruwa na gabas.
“Wayar da kan ‘yan Najeriya akan muhimmancin wadannan matakai da Najeriya ta dauka, musamman ta kafafen sada zumunta.
“Tura gaggun sojojin Najeriya da jami’ai don tilasta bin ka’idojin.”


