Sanata Kawu Sumaila ya ja hankalin Tinubu kan illar yakar Nijer

Date:

Sanata Abdulrahman Kawu Sumaila na Jam’iyar NNPP mai wakiltar Kano ta kudu ya kasance mai magana da yawun sanatocin arewa tun kwanakin Baya. Bayan kama aiki, kawu ya bayyanawa manema labarai akan matsayar kungiyar sanatocin arewa kan maganar da ECOWAS suke akan yakar jamhuriyar Nijer.

Sanata Kawu yace “Mu sanatocin arewa bama goyon bayan yakar jamhuriyar Nijer, kuma muna kira ga ECOWAS karkashin jagorancin shugaba Tinubu da ayi wannan abun cikin masalaha amma bah Yaki bah. Domin Yaki bah Alkhairi bane, Zai Janyo asarar rayuka da dukiyar al’umma wadanda basuji ba basu gani ba.

Haka zalika, jihohin arewacin Najeriya bakwai (7) ne sukayi makokantaka da jamhuryar Nijer kamar Haka:
KATSINA, ZAMFARA, SOKOTO, KEBBI, YOBE, BORNO da JIGAWA.

Duk wannan jihohin Arewacin Najeriya ne, kuma muddin za ayi yaki da kasar Nijer sai al’ummar jihohin sun cutu ta fannoni da dama. Daman chan wasu daga ciki suna fama da rashin tsaro, kaga kenan za’a rura wutar rashin tsaro a wannan yankunan…”
Sanata Kawu Sumaila dai tsohon dan majalisar wakilai ne kwararre wanda ya wakilci kananan hukumomin Sumaila da Takai kuma tsohon mai bawa tsohon shugan kasa Muhammadu Buhari shawara kan abunda ya shafi majalisar.

Share post:

Subscribe

spot_imgspot_img

Popular

More like this
Related

Quarter 1 2026: Lagos, Abuja, Rivers, Delta Lead States with Highest Debt Increase

Nigeria’s subnational domestic debt rose in the first quarter...

Anambra Bizman Abductors Demand N1.5bn Ransom

Gunmen who kidnapped the chairman of Jezco Group, Chief...

State Police Bill: FG Extends Deadline, Seeks More Consultation

The Federal government has extended the deadline for the...

Osun Govt Drags Fadahunsi to Court over “Kill Accord Members” Threat

The Osun State Government has approached the High Court...