Kotun Birtaniya ta kwace kudaden tsohon gwamna Ibori

Date:

Wani alƙali a birnin London ya ba da umarnin ƙwace dala miliyan 130 a hannun tsohon gwamnan Najeriya James Ibori, kuɗaɗen da ake zargin sato su ya yi har aka ɗaure shi a gidan yari.

Lauyan ya ba da umarnin ne a ranar Juma’ar da ta gabata.

Umarnin yana ɗaya daga cikin manyan matakan ƙwace kuɗi da aka yi wa wani mutum a tarihin shari’a na Birtaniya baya-bayan nan.

Mista Ibori ya yi gwamnan jihar Delta mai arzikin man fetur tsawon shekara takwas inda rahotanni suka ce ya saci kudaden da aka tanada domin gudanar da ayyukan ci gaban jihar.

A shekarar 2011 ne aka tasa ƙeyar sa daga Dubai zuwa Birtaniya, kuma an tuhume shi da laifin halarta kuɗin haram da suka kai miliyoyin daloli a wata kotun Birtaniya.

A 2012 ne, tsohon gwamnan ya amsa laifuka 10 da suka hada da zamba da halarta kuɗin haram sannan kuma an yanke masa hukuncin daurin shekara 13 a gidan yari.

Yanzu dai, an umarci Mista Ibori ya yafe kudin nan take ko kuma a ɗaure shi na tsawon shekara takwas.

A halin yanzu dai, tsohon gwamnan yana Najeriya. Rahotanni sun ce ya sha alwashin ɗaukaka ƙara a kan umarnin ƙwace kuɗaɗe..

Babu tabbas ko gwamnatin Najeriya za ta ba da haɗin kai wajen aiwatar da wannan oda. Tsohon gwamnan dai yana da kusanci da Bola Ahmed Tinubu, shugaban Najeriya a yanzu. Tun hawansa mulki a watan Mayu, ya karbi bakuncin Ibori sau biyu a fadarsa, tare da wasu tsoffin gwamnoni.

Hukuncin Mista Ibori a 2012 ya samu lambar yabo sosai lokacin a matsayin wani abin tarihi a yaƙi da cin hanci da rashawa a Biritaniya da Najeriya.

Akwai tsammanin cewa kudaden da za a kwace za a mayar da su Najeriya idan har shari’a ta yi nasara.

Share post:

Subscribe

spot_imgspot_img

Popular

More like this
Related

Quarter 1 2026: Lagos, Abuja, Rivers, Delta Lead States with Highest Debt Increase

Nigeria’s subnational domestic debt rose in the first quarter...

Anambra Bizman Abductors Demand N1.5bn Ransom

Gunmen who kidnapped the chairman of Jezco Group, Chief...

State Police Bill: FG Extends Deadline, Seeks More Consultation

The Federal government has extended the deadline for the...

Osun Govt Drags Fadahunsi to Court over “Kill Accord Members” Threat

The Osun State Government has approached the High Court...