Kwamitin raba KUDADEN hadaka na kasa zai raba kimanin naira tiriliyan 2 a watan Yuli, karo na farko a tarihi, a matsayin kason da matakai uku na gwamnati za su samu a matsayin rabon su,. Sakamakon cire tallafin man fetir da a ka yi.
Wannan dumbin kudi da, da ba a cire tallafin ba, zai salwanta a wancan 6angare a wata daya, yanzu zai tafi zuwa ga inganta rayuwar al’umma.
Gwamnatocin jihohi da na kananan hukumomi yanzu za su samu wadatattun kudi da za su biya albashin maaikatan su da Kuma ‘yan fansho. Gwamnatocin za su zama masu wadatar da zasu rage kar6i bashi, Kuma za su iya biyan mafi kankantar albashi Kuma su bayar da isassun kudaden da za a tabbatar da ci gaba a 6angarorin ilimi, lafiya da sifiri.
Duba da wannan, dole yanzu a saka Ido a Kan gwamnatocin jihohi da kananan hukumomi domin tabbatar da gaskiya da amana wajen gudanar da dukiyar al’umma. Gudanarwa ingantacciya tana da muhimmanci a matakin jihohi da kananan hukumomi.
Rahotanni sun nuna cewa daga wannan adadi na naira tiriliyan 2, kusan naira tiriliyan 1 za a rabawa matakan gwamnati guda 3, ragowar tiriliyan daya za a saka su a wani sabon asusu da za a Rika amfani da su wajen gudanar da ayyukan bai daya da zasu rage radadin da cire tallafin man fetir ya gadar wa da talakawa.


