Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano, PCACC, ta bayyana cewa ta dauki hayar fitaccen lauyannan dan rajin kare hakkin bil’adama, Femi Falana (SAN), don ya taimaka wajen kalubalantar karar da tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje, ya shigar, na dakatar da binciken da hukumar ke yi kan bidiyon sa na karbar cin hancin dalar Amurka.
Lauyan hukumar Usman Fari ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a bayan da kotu ta dage sauraron karar zuwa ranar 25 ga watan Yuli. Ya tabbar da cewa babban lauyan zai iso Jihar Kano kuma zai jagoranci sauran lauyoyin guda shida.
Dage shari’ar ya biyo bayan lauyan Ganduje, Basil Hemba da ya shaidawa kotun cewa suna bukatar karin lokaci domin amsa karar da hukumar ta shigar.
“ Lauyan hukumar Usman Fari ya shaidawa kafafen yada labarai cewa A ranar 25 ga watan Yuli, babban lauyan nan, Femi Falana (SAN) zai jagoranci lauyoyin a madadin mutane shida. Hukumar ta sa shi ya jagorance mu a kan lamarin kuma a shirye muke mu ci gaba da shari’ar,” Fari ya ce yayin da yake zantawa da manema labarai.
Aminiya ta tattaro cewa da safiyar Juma’a ne aka bukaci babban lauyan ya isa Kano domin ya jagoranci tawagar amma ya samu wasu kalubale da jirgin nasa.
Idan za a iya tunawa, tsohon gwamnan ya shigar da karar ne don neman “tabbatar da muhimman hakkokinsa na dan Adam na shari’a na gaskiya, na sirri da kuma na iyali” a gaban babbar kotun tarayya da ke Kano bayan da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta bayyana cewa ta gayyace shi da ya gurfana a gabanta domin amsa tambayoyi dangane da binciken da ta yi kan faifan bidiyo da aka yi zargin cewa yana cusa kudin dalar Amurka wanda ya jawo zargin da ake masa na karbar cin hanci da rashawa.


