Tsohon gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje ya zama sabon shugaban jam’iyyar APC na kasa.
An zabe shi ne a taron kwamitin zartaswa na kasa karo na 12 da aka gudanar a Abuja.
Nadin na tsohon gwamnan Kano Ganduje ya biyo bayan murabus din Sanata Abdullahi Adamu ne a watan jiya. Jaridar Boss Newspapers ta samu labari cewa Shugaba Bola Tinubu ne ya nuna sha’awar Ganduje ya gaji Adamu. Haka kuma, jamiyyar ta APC ta tabbatar da Sanata Ajibola Bashiru, tsohon kakakin majalisar dattawa, a matsayin sakataren jam’iyyar na kasa.
Taron na NEC ya shaida halartar mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, da gwamnoni da dama, da manyan jiga-jigan jam’iyyar tare da shugaba Bola Ahmed Tinubu.


