Laolu Akande, mai magana da yawun tsohon mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya bayyana dalilin rashin halartar tsohon mataimakin shugaban kasa a taron jam’iyyar All Progressives Congress (APC).
A cikin wata sanarwa da Akande ya fitar, ya ce Osinbajo ba zai iya halartar taron ba a ranar Larabar da ta gabata, saboda yayi balaguru wajen Najeriya ne saboda wasu ayyuka da ya sa a gaba.
“A cikin wasikar neman gafara saboda rashin zuwansa da ya aike wa mukaddashin shugaban jam’iyyar (Abubakar Kyari), tsohon mataimakin shugaban kasar ya bayyana cewa ya riga ya fita kasar waje domin wasu muhimman ayyuka, a lokacin da ya samu gayyatar taron. ”
Bayanin a wani bangare ya zo kamar haka:
“Hakika ya soke wasu alkawurran da ya yi a kasashen waje domin halartar tarukan jiga-jigan jam’iyyar guda biyu da aka shirya a baya wadanda daga bisani aka dage su.
“Yayin da yake yi wa jam’iyyar fatan alkhairi, ya bayyana kudurinsa na bawa jam’iyyar cikakken goyon baya da kuma samun halartar tarurruka da ayyukan jam’iyyar nan gaba.”
Osinbajo ya kasance mataimakin shugaban Najeriya daga watan Mayu na shekarar 2015 zuwa Mayu 2023 a lokacin gwamnatin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Farfesan lauyan ya tsaya takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC a watan Yunin 2022 amma ya sha kaye a hannun tsohon gwamnan jihar Legas, Bola Tinubu.
Wani abin sha’awa shi ne, Osinbajo ya kasance daya daga cikin manyan lauyoyi na yankin Yorubawa kuma kwamishinan shari’a na Legas a lokacin da Tinubu yake gwamnan Legas tsakanin 1999 zuwa 2007.


