Connect with us

News in Hausa

Kungiyar NLC ta gudanar da zanga-zanga a Kano kan tallafin man fetur

Published

on

Mambobin kungiyar kwadago ta Najeriya NLC da TUC sun gudanar da zanga-zangar nuna adawa da cire tallafin man fetur a Kano.

Masu zanga-zangar dai sun yi dandazo ne a harabar dakin karatu na jihar Kano kafin su wuce kofar gidan gwamnatin jihar, inda suka bukaci hukumomin da su dakatar da cire tallafin man fetur.

Da suke rera wakokin hadin kai a lokacin da suke tattaki, masu zanga-zangar suna dauke da alluna masu dauke da ta’ke kamar haka: “Ku daina nuna mana kiyayya, ku makiyan alumma ne, ku daina munanan manufofi. Biyu ga watan Agusta ita ce ranar!”

“Don haka, a cikin mutane miliyan 200, mutane miliyan 133 talakawa ne. Amma duk da haka, masu mulki basu fasa babakere, handama da azurta kansu ba.”

A kasa ga hotunan zanga-zangar.

Continue Reading
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

News in Hausa

Kotu za ta yanke hukunci a kan zaben gwamnan Kaduna

Published

on

By

Kotun sauraron kararrakin zaben gwamna da ke jihar Kaduna za ta yanke hukunci a yau Alhamis 28 ga Satumba, 2023.
Jaridar The Boss ta samu labarin cewa kotun zata zartar da hukuncinta ne ta hanyar Zoom, a inda zata ayyana hukunci kan karar da jam’iyyar PDP da dan takararta, Isah Mohammed Ashiru Kudan suka gabatar a gabanta na neman korar Uba Sani a matsayin gwamnan jihar. Sani ya kasance dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a lokacin zaben.
Jaridar The Boss zata kawo cikakkun bayanai daga baya…

Continue Reading

News in Hausa

Kungiyar Kwadago Zata Shiga Yajin Aikin Sai Baba Tagani

Published

on

By

Kungiyoyin kwadago na NLC da TUC ta sanar da kudirinda na shiga aikin sai baba tagani a ranar Talata mai zuwa 3 ga watan Oktoba 2023. Hakan ya biyo bayan zaman tattaunawa da shugabannin kungiyoyin sukayi a yau Talata a Abuja.
Daya daga cikin korafin kungiyoyin nada alaka da halin tsananin wahala da yan Najeriya suke ciki, da kuma gazawar gwamnatin tarayya bisa alkawarin kawo tsare-tsare na rage radadi ga al’umma.

Continue Reading

News in Hausa

Gwamnan Kano Yusuf Na Jamiyyar NNPP Ya Daukaka Kara

Published

on

By

Gwamnan Jihar Kano, Alh Abba Kabir Yusuf da jamiyyar NNPP sun tafi kotun daukaka kara dake Kaduna domin daukakak kara kan hukuncin da kotun sauraren Korafe-Korafen Zaben gwamna a Jihar Kano ta Yanke a Bisa Kuskure.

Jaridar Boss ta tattaro bayani cewa gwamnatin Kano ta hayo manyan lauyoyi da zasu tsaya Mata a Kotun daukaka Kara da ke Kaduna.

Ga Jerin Gogaggun lauyoyin Masu Rike da Mukamin SAN ( Senior Advocate of Nigeria) Har Guda BAKWAI (7), Ga Jerin Sunayen Su Nan Akasa.

1. Chief Awomolo (SAN)
2. Chief John Beisha (SAN)
3. Chief Lawan Rabbana (SAN)
4. A . J Owonikoko (SAN)
5. Akomolafe (SAN)
6. Abdulhamid Muhammed (SAN)
7. Eyitayo Fatogun (SAN)

Continue Reading

Trending

%d bloggers like this: