Connect with us

News in Hausa

Gwamna Sule Yace Dubu Takwas kudi ne Mai Tarin Yawa a Wajen Wasu

Published

on

Gwamna Abdullahi Sule na Jihar Nasarawa ya kare tallafin Naira 8,000 da Gwamnatin Tarayya ke shirin kawowa don rage radadin cire tallafin man fetur a tsakanin talakawa.
Da yake magana a gidan Talabijin na Channels sashen siyasa a jiya Juma’a, Gwamnan ya ce N8,000 wani adadi ne mai yawa ga iyalai da dama da ke fama da talauci wadanda ba kasafai ake samun irin wannan ba a cikin wata guda.

Ya tunatar da cewa iyalai da yawa ne suka ci gajiyar N5,000 da aka raba a baya a matsayin agaji, yana mai cewa matakin na yanzu ya dace.
“Muna raba N5,000 ne kawai kuma na yarda cewa akwai mutane da yawa da ke jiran wannan N5,000 duk wata. Lallai akwai wasu al’ummomi da suka iya ba da gudummawarsu kuma sun iya yin abubuwa da yawa a cikin al’ummominsu daban-daban.”

“Don haka, Naira 8,000 na iya zama ba kudi mai yawa ba ga wasu mutane, amma yana da yawa ga wasu da yawa daga cikin iyalai marasa galihu da ba sa ganin N8,000 duk wata. Don haka, abu daya kawai shi ne mu tantance wadannan iyalai.”
Shugaban kasa, Bola Tinubu, ya bayar da umarnin sake duba kudaden tallafin Naira 8,000, biyo bayan harzuka da aka yi a fadin kasar.

Continue Reading
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

News in Hausa

Shin ko karfin siyasar ta Wike tasamu rauni?

Published

on

By

A cikin dama guda daya da Gwamnan Ribas Siminalaya Fubara ya samu:

1. Ya kori shugaban ma’aikata na fadar Gwamnatin jihar, wanda Wike ne ya nada shi.

2. Ya cire dukkan shugabannin kananan hukumomi guda ashirin da uku ba jihar baki daya, wanda duk Wike ne ya kawo su.

3. Ya rushe majalisar zartarwar jihar, wadda ta kunshi Kwamishinoni, wanda fiye da rabinsu Wike ne ya kawo su.

4. Ya canja Kakakin Majalisar dokokin jihar wanda shima Wike ne ya kawo shi.

5. Ya dakatar da babban jojin jihar wanda shima Wike ne ya kawo shi.

Wannan karamin misali ne na irin karfin da kujerar Gwamna ta ke da shi a Najeriya. Wike ya manta duk abinda yake yi saboda yana rike da kujerar Gwamnan ne, yau damar da ya samu yayi abinda yaga dama ita wani ya samu ya lalata masa siyasa cikin kankanin lokaci.

Wike ya tarawa kansa abokan fada da yawa, kuma ba zai iya ba. Domin da alama Sim Fubara ya kawo karshen tasirin da Wike yake ganin yana da shi a siyasar Najeriya. Kama-ta-dinu tu-danu.

Continue Reading

News in Hausa

Kotu za ta yanke hukunci a kan zaben gwamnan Kaduna

Published

on

By

Kotun sauraron kararrakin zaben gwamna da ke jihar Kaduna za ta yanke hukunci a yau Alhamis 28 ga Satumba, 2023.
Jaridar The Boss ta samu labarin cewa kotun zata zartar da hukuncinta ne ta hanyar Zoom, a inda zata ayyana hukunci kan karar da jam’iyyar PDP da dan takararta, Isah Mohammed Ashiru Kudan suka gabatar a gabanta na neman korar Uba Sani a matsayin gwamnan jihar. Sani ya kasance dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a lokacin zaben.
Jaridar The Boss zata kawo cikakkun bayanai daga baya…

Continue Reading

News in Hausa

Kungiyar Kwadago Zata Shiga Yajin Aikin Sai Baba Tagani

Published

on

By

Kungiyoyin kwadago na NLC da TUC ta sanar da kudirinda na shiga aikin sai baba tagani a ranar Talata mai zuwa 3 ga watan Oktoba 2023. Hakan ya biyo bayan zaman tattaunawa da shugabannin kungiyoyin sukayi a yau Talata a Abuja.
Daya daga cikin korafin kungiyoyin nada alaka da halin tsananin wahala da yan Najeriya suke ciki, da kuma gazawar gwamnatin tarayya bisa alkawarin kawo tsare-tsare na rage radadi ga al’umma.

Continue Reading

Trending