Majalisar Dattijai a halin yanzu na Ganawar Sirri Akan jerin sunayen Sababbin Ministoci da shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya turamusu domin su tantance su a karkashin jagorancin shugaban Majalisar Dattijai Sanata Godswill Akpabio.
Sun Fara tattaunawar da misalin karfe 11:59 a.m bayan Sanata Opeyemi (APC, Ekiti ta tsakiya) Bamidele ya bada sanarwar umarnin.
Wata majiya Mai karfi tayi nuni ga Boss Newspaper Hausa cewa jerin sunayen ya janyo kace-nace tsakanin sanatocin, Wanda hakan ya jawo bukar tattaunawar ta gaggawa a tsakaninsu.
Zamu iya tinawa a jiya Laraba ba shugaban Majalisar Sanata Akpabio yayi wata ganawa Mai tsayi da masu ruwa da tsaki akan al’amarin.
Majiyar ta yi nuni da cewa tuni jerin sunayen yana tare da shugaban Majalisar, inda ake zaton zai karantosu bayan wannan tattaunawa da sukeyi kokuma sati mai zuwa kasancewar babu zaman majalisar a gobe Juma’a.


