Azamanta na ranal Laraba 19/7/2023, Majalisar Wakilan ta yi watsi da qudirin da aka bijiro dashi domin dakatar da karin farashin man fetur da yafara a jiya Talata a fadin Najeria. Kudirin ya bukaci majalisar da ta tilasta dawo da tsohon farashin man fetur din a #537 duk lita guda.
Majalisar zata gabatar da bincike akan qarin da akayi cikin gaggawa, da Kuma tasirin da qarin zai haifar ga zirga zirgan ababen hawa a qasa bakidaya.
Dan Majalisa Ikenga Ugochinyere, yagafatar da qudurin cewa Mele Kyari, Managern director na babbar maaikatar gwamnati mai kula da abubuwan da suka shafi man fetur a kasa Najeriya. Ya bukaci da su bayyana a gaban kwamitin majalisar domin yimusu bayani game da dalilan da yasa akayi qarin.
Kwamitin Majalisar ya ci alwashin mai da hankali wajan Samar da hanyoyin daza a raba tallafi ga ‘yan Nigeria domin rage radadin da cire tallafin man ya haifar.


