Ganduje Zai Zama Shugaban Jama’iyyar APC Na Kasa

Date:

Tsohon Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje na shirin zama shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa.

Sakamakon rikice-rikicen cikin gida da jam’iyyar APC ke fuskanta a jihohi da dama da ma a matakin kasa, shugaba Bola Tinubu na neman wanda ya cancanta, gogaggen hannu don sake fasalin jam’iyyar, a cewar wata majiya mai tushe daga fadar shugaban kasa.

A cewar majiyar, mai yiwuwa shugaban kasar ya zabi Ganduje ne saboda ya yi imanin cewa tsohon gwamnan yana da halayen da yake nema a matsayin shugaban jam’iyyar.

Jaridar Boss ta Hausa ta samu labarin cewa shugaban kasar ya aika da jakadu domin shawo kan tsohon Gwamna Ganduje, wanda tuni ake shirin nada shi minista.

Mutane uku na gwamnan jihar Imo, shugaban kungiyar gwamnonin ci gaba, gwamnan jihar Kwara, Abdulraham Abdulrasaq, da gwamnan jihar Ogun Dapo Abiodun, aka tura zuwa ga Ganduje.

Rahotanni sun bayyana cewa, tsohon Gwamnan ya amince da yin aiki domin amfanin jam’iyyar da kuma kasa baki daya.
Zamu iya tinawa tsohon Shugaban Jamiyyar ta APC Abdullahi Adamu ya sauka daga kujerarsa ta shugabancin jamiyyar kwanaki kadan da suka gabata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

spot_imgspot_img

Popular

More like this
Related

UK PM Burnham Unveils 10-Year Plan, Begins Cabinet Overhaul

The new British Prime Minister, Andy Burnham, on Monday,...

Where’s the Nigeria’s Oil Metering Fund?

By Boma Lilian Braide Esq A single administrative letter dated...

ADC Tells Tinubu to Resign As World Bank Reveals 139million Nigerians Live in Poverty

The African Democratic Congress (ADC) on Saturday asked President...

Dominican University Hails Peter Obi on 65th Birthday

The Dominican University, Ibadan, has paid glowing tribute to...