Kotun sauraron kararrakin zabe a Kano sun fallasa yan siyasa

Date:

Zarge-zargen da ke fitowa daga kotun sauraron kararrakin zaben ‘yan majalisar dokokin jihar Kano a baya-bayan nan na cewa wasu lauyoyi na neman yin tasiri ga alkalan da kudi a shari’o’i da dama da ke gabansu ya haifar da cece-kuce tare da zarge-zarge tsakanin jam’iyyu da masu ruwa da tsaki a fannin shari’a kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Yayin da kungiyar lauyoyin Najeriya NBA, ta rubutawa kotun bukatar ta akan ta bayyana musu sunayen mambobinta da ke da hannu a zarge-zargen cin hanci da rashawa, ta daya bangaren kuma manyan jam’iyyu biyu a jihar na ci gaba da musayar kalamai inda kowacce daga ciki ke nuna abokiyar hamayyar ta da yatsa inda kowacce ke zargin dayar nada hannu wajen badakalar cin hancin.

Jaridar The Boss ta tattaro cewa mai shari’a Flora Ngozi Azinge, shugabar kwamiti na 1 na kotun a zamanta na ranar Talata ta koka kan abin da ta bayyana a matsayin wani lamari mai tayar da hankali wanda a cikinsa lauyoyin da ke da kararrakin da ke gaban kwamitin na tuntubar ta da mambobin kwamitinta domin yin domin shawo kansu su karkarta kansu yayin yanke hukunci da kuma yin almundahana a shariar baki daya.

Amma babu tabbacin cewa sakatariyar kotun ta bayar ko taki bayar da cikakken bayani kan abin da ya faru a ranar Talata din. A yayin da ake ci gaba da shari’ar, mai shari’a Azinge ta yi wannan zargin ne a bayyana a gaban kotu…

Share post:

Subscribe

spot_imgspot_img

Popular

More like this
Related

Quarter 1 2026: Lagos, Abuja, Rivers, Delta Lead States with Highest Debt Increase

Nigeria’s subnational domestic debt rose in the first quarter...

Anambra Bizman Abductors Demand N1.5bn Ransom

Gunmen who kidnapped the chairman of Jezco Group, Chief...

State Police Bill: FG Extends Deadline, Seeks More Consultation

The Federal government has extended the deadline for the...

Osun Govt Drags Fadahunsi to Court over “Kill Accord Members” Threat

The Osun State Government has approached the High Court...