Tsohon dan takarar shugaban kasa Yabagi Sani ya caccaki shugaba Tinubu kan ingancin sabbin ministoci da ya zaba, inda ya zargeshi da dawo da mutanan da yan Najeriya suka ki amincewa dasu a fagen zabe don su mulkesu ta bayan fage a matsayin ministoci.
A tattaunawar sa da gidan talabijin na channels, yace:
“Na ji takaici kwarai saboda Shugaba Tinubu yana nuna halaye dabam da yadda nake tsammaninsa, ‘yan Najeriya na cewa sake dawo da mutanan da al’umar Najeriya basu amunta da su ba ba abin da ya kamata Shugaba Tinubu ya yi bane. Da yawa daga cikin mutanen da ya sanya a matsayin ministoci mutane basu karbesu ba. Ta yaya za ku dawo da su ta bayan gida ku ce dole ne su jagoranci jama’a? Wannan bashi ne tsarin da duk dan Najeriya mai so cigaba keso a tafi a kai ba.”
Yabagi Sani, shi ne Shugaban kungiyar IPAC na kasa.


