Tsohon Gwamna Ganduje da Dan takara Gawuna Sun tofa nasu bayan Hukuncin Kotu.
A cewar tsohon gwamnan jihar kano kuma shugaban jam iyyar APC ta kasa, Dr Abdullahi Umar Ganduje ya nuna godiyarsa ga Ubangiji bisa nasarar da yabasu a shariar da kotun sauraron kararrakin Zabe ta gudanar a jiya.
Ganduje yabayyana cewa suna godiya ga magoya bayansu tare da alkawarta musu cewa zasu Dora ayyukansu daga inda suka tsaya a baya.
Dan takarar gwamnan na APC a zaben na da ya gabata a watan Fabrairu na 2023 Dr Nasiru Yusuf Gawuna ya jaddada cewa Zai yiwa al’ummar Kano adalci.
Gawuna ya bayyana godiyarsa bisa nasarar da yayi a kotu inda yace zai Dora ayyuka alkhairi kamar yadda ya gada daga ubangidansa.


