Kwamitin shiga tsakani na Ecowas ya sake koma wa Jamhuriyar Nijar, a ƙoƙarin ganin an shawo kan dambarwar siyasar ƙasar ta hanyar lumana.Tawagar ƙarƙashin jagorancin tsohon shugaban mulkin soja na Najeriya, Abdulsalami Abubakar, ta samu tarba daga Firaministan Nijar Ali Lamine Zeine, wanda sojoji suka naɗa.
Juyin Mulkin Nijar: Kwamitin shiga tsakani ya zauna da firaminista
Date:


