Dan majalisar tarayya, Bashir Gorau ya yunkura kan kawo karshen matsalar tsaro a Sokoto

Date:

Hazikin matashin dan majalisar tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Goronyo da Gada da ke jihar Sokoto yayi wata ganawa da babban hafsan sojojin Najeriya Janar Taoreed Abiodun Lagbaja a yammacin yau Litinin.

Tattaunawar tasu dai tafi karkata kan yanda za a kawo karshen matsalar tsaro a wasu yankuna daga inda yake wakilta dama wasu sassan na jihar Sokoto baki daya, kamar yadda ya wallafa a shafukansa na kafafan sadarwa kamar haka:

“Nayi ganawa mai gamsarwa tare da babban Hafsan Sojojin kasa, Janar Taoreed Abiodun Lagbaja, inda muka tattauna hanyoyin magance matsalar rashin tsaro da ‘yan bindiga a Kananan Hukumomin Goronyo da Gada da kuma Sokoto ta Gabas baki ɗaya. Mun tattauna kafa sansanin Sojoji a Kwanar Mahalba, mazaunin Sojoji a Gada, da kuma shiga Dajin Gundumi domin kawarda ɓata-gari. Ina farin cikin cewa Janar Lagbaja ya himmatu wajen tabbatar da tsaronmu kuma yana neman goyon bayanmu, bayanai, da addu’o’in ga Sojoji domin samun nasarar wannan muhimmin aiki…”

Share post:

Subscribe

spot_imgspot_img

Popular

More like this
Related

Voice of Emancipation: The True Cost of Freedom

By Kayode Emola For many millennia, humanity has chased one...

Atiku vs Tinubu: Why Tinubu Will Lose the 2027 Election

By Dr. Sani Sa'idu Baba Let me begin with this...

PRIDE: The Plague That Drives, and Entombs the Proud

By Tolulope A. Adegoke PhD Pride is the only fortress...

Solemn Farewell for Ooni’s Brother, Prince Adetunji Ogunwusi in Ile-Ife

By Eric Elezuo The two days set aside for the...